Kungiyar tarayyar Afirka ta AU da kasar Habasha, sun jinjinawa kwazon kasar Sin don gane da tallafi, da rawar da take taka wa wajen ganin an kai ga nasarar wanzar da zaman lafiya da samar da tsaro a kasashen Afirka.
Da yake tsokaci kan hakan, yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan, babban mashawarcin hukumar zartaswar AU mista Frederic Gateretse-Ngoga, ya ce Sin ta wanzar da matsayinta na mai taimakawa nahiyar Afirka, ta hanyar shiga a dama da ita a ayyukan kandagarkin tashe-tashen hankula, da shiga tsakani da ayyukan wanzar da zaman lafiya.
A nasa bangare kuwa, kwamishinan hukumar gudanar da shawarwari ta kasar Habasha Yonas Adaye, cewa ya yi kasar Sin na iya tallafawa nahiyar Afirka da dabarun kwarewa, da cin gajiyar dunbin albarkatun su, ta hanyar fasahohin ta na zamani, irin su na tsaron yanar gizo da fasahar kwaikwayon tunanin bil Adama ko AI, don dakile yiwuwar kaiwa na’urori masu kwakwalwa farmaki. (Mai fassara: Saminu Alhassan)