An gabatar da bikin bude nune-nune tarihin al’adun kasar Sin ga duniya mai taken “Journey Through Civilisation” na rukunin gidajen talabijin da rediyo na kasar Sin CMG, a hedkwatar MDD dake birnin New York.
An fara gabatar da nune-nunen ne daga ranar 26 ga wata, kuma zai ci gaba har zuwa 7 ga watan Yuli. Haka kuma, za a gabatar da shi daga watan Yuni zuwa Nuwamba, a kasashe kamar Amurka da Birtaniya da Masar da Kenya da Peru da sauransu.
Shugaban CMG Shen Haixiong, ya bayyana cikin wani jawabi da ya gabatar ta kafar bidiyo cewa, CMG zai daukaka burinsa na yada labarai da karfafa musayar al’adu tsakanin al’ummun kasa da kasa da bayar da gudunmowa wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil Adama. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)