A yau Litinin aka kaddamar da gasar tsara bidiyo ta matasan Sin da Afrika mai taken “Great to Meet You” ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, wanda ke zaman wani yunkuri na ganin kyan bangarorin biyu da kuma kulla abota.
Manufar wannan gasa ita ce, amfani da gajeren bidiyon da aka tsara wajen samar da dandalin musaya da koyo daga juna tsakanin matasan Sin da Afrika, da bayyana salon matasan Sin da Afrika tare da inganta dorewar abota tsakanin Sin da Afrika. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp