A yau Lahadi, aka kaddamar da wani sabon gini irinsa na farko na zamani, da ba ya fitar da hayakin carbon ko kadan, a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin. Wannan wata gagarumar nasarar ce a kokarin kasar na kawar da fitar da hayakin carbon baki daya.
Yayin da ake bukatar kilowatta sa’a 6,000 a kowacce rana, ginin ofishin mai tsawon mita 117 na dauke da kayayyaki na fasahohin zamani masu inganci da suka maye gurbin masu gurbata muhalli da makamshi mai tsafta 100 bisa 100.
Ba kamar sauran gine-ginen da aka saba gani da ake shimfida musu allunan sola a sama ba, a wannan gini akwai bangon gilas dake samar da lantarki daga hasken rana a bangarorin gabas da kudu da yammacinsa.
Wannan yana samar da lantarki da rage asarar makamashi da kuma samar da kaso 25 na bukatun makamshi na ginin. Haka kuma zai kai ga rage fitar hayakin Carbon tan 500 a shekara.
Baya ga haka, ginin na amfani da tsoffin baturan motoci masu amfani da lantarki, wajen adana makamashi. Ana amfani da irin wadannan batura guda 14 wajen adana rarar makamashin da ake samu daga bangon gilas mai zukar hasken rana da samar da makamashi mai tsafta a lokaci mafi samun hasken rana, a farashin yuan 0.22 kwatankwacin $0.031, kan kilowatt 1 a kowacce sa’a. Kuma za a yi amfani da makamashin da aka adana a lokacin da ake bukatar lantarki mai yawa ko kuma lokacin da ake da karancin hasken rana domin daidaita bukatar makashi. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp