A jiya ne, aka kaddamar da kauye na farko na gwajin dabarar raya aikin gona da ta rage talauci bisa hadin gwiwar Sin da Afirka a kasar Kenya, a kauyen Matangitiza dake garin Nakuru na kasar.
A jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo yayin bikin kaddamarwar, mataimakin shugaban jami’ar aikin gona ta Nanjing ta kasar Sin, Hu Feng, ya bayyana fatan ganin kauyen ya zama abin koyi a fannin hadin gwiwar Sin da Afirka, ta yadda za a sa kaimi ga kokarin yayata fasahohin aikin gona masu inganci na kasar Sin a kasar ta Kenya, da ma nahiyar Afirka baki daya.
A nashi bangare, farfesa Richard Mulwa, mataimakin shugaban jami’ar Egerton ta kasar Kenya, ya bayyana a cikin sakonsa ta kafar bidiyo cewa, yana fanin yin amfani da damar kaddamar da kauye na gwaji, don shigo da karin fasahohin ci gaba na aikin gona daga kasar Sin, da zurfafa huldar hadin kai dake tsakanin jami’arsa da jami’ar aikin gona ta Nanjing ta kasar Sin, gami da karfafa zumuntar dake tsakanin bangarorin Afirka da Sin. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp