An kaddamar da makon nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), ranar Juma’a a Qingdao mai taken “Duniya ta hadu ta hanyar haske da inuwa a Qingdao”, lamarin da ya mayar da birnin zuwa cibiyar musayar al’adu da bukukuwan nuna fina-finai.
Shirin wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da gwamnatin birnin Qingdao suka shirya, da taimakon hukumar kula da shirya fina-finai ta Sin, zai gudana tsawon mako guda, inda ya hada mashirya fina-finai da jagororin masana’antar da jami’ai kamar sakatare janar na SCO da shugabannin CMG da manyan jami’an diplomasiyya da masu wakiltar al’adu da taurarin fina-finai da masu tsara shirye-shirye a shafukan sada zumunta da ‘yan kallo daga kasashe mambobin kungiyar SCO, domin zurfafa musayar al’adu da lalubo damarmakin hadin gwiwa a masana’antar shirya fina-finai. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp