Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin halartar taron shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pacific (APEC) karo na 32 a Koriya ta Kudu da kuma ziyarar aiki a kasar Koriya ta Kudu, an kaddamar da nuna muhimman shirye-shiryen talabijin da fina-finai na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a membobin APEC. Za a watsa shirye-shiryen fiye da goma a manyan kafofin watsa labarai 22 a kasashe 14 na yankin Asiya da tekun Pacific, ciki har da Australia, Kanada, Chile, Indonesia, Koriya ta Kudu, Peru, Rasha, Thailand, da Amurka.
Babban darektan CMG Shen Haixiong, ya fada a cikin wani sakon bidiyo cewa, ana fatan wadannan shirye-shiryen talabijin da fina-finai za su iya taimaka wa masu kallo da sauraro a yankin Asiya da tekun Pacific wajen fahimtar hikimar shugaba Xi a fannin shugabanci, da ci gaban kasar Sin a sabon zamani, da al’adun kasar Sin, da kuma bunkasa ci gaban zaman lafiya, da hadin gwiwa mai amfanarwa ga dukkan bangarori, da kuma samun wadata a tsakanin kasashen Asiya da tekun Pacific. (Abdulrazaq Yahuza Jere)












