A yau Litinin 1 ga watan Disamba ne aka kaddamar da taron fahimtar kasar Sin na kasa da kasa na shekarar 2025, a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin. Taken taron shi ne “Sabon tsari, da sabon ci gaba, da sabon zabi dangane da zamanantarwa irin ta kasar Sin, da tafiyar da harkokin kasa da kasa”.
Taron ya samu halartar mashahuran ‘yan siyasa, da masana, da shugabannin bangarori daban daban, da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa. An kuma maida hankali ga shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 na kasar Sin da tasirinsa a duniya, kana an tattauna sabon tsarin kirkire-kirkire, da samun ci gaba kan zamanantarwa irin ta kasar Sin, da samar da sabuwar dama ga zamanantar da duniya, da yin kokari wajen aiwatar da shawarar duniya kan tafiyar da harkokin duniya da sauransu.
Kwamitin shirya taron ya ce wakilai kimanin 200 daga kasashe da yankuna 72 sun halarci taron. A cikin adadin kashi 70 cikin dari sun zo ne daga kasashe masu tasowa, kana kashi 70 cikin dari sun halarci taron a karo na farko, yayin da jimillar adadin mutanen da suka halarci taron a wannan karo ya kai kimanin 800. (Zainab Zhang)














