Bankin Stanbic na kasar Namibia, ya kaddamar da tsarin biyan kudi da kudin Sin watau CIPS, inda ya zama banki na farko a kasar da ke samar da wannan hidima, a wani yunkuri na saukaka hada-hadar kudi kai tsaye da kudin Sin Renminbi (RMB) da kuma inganta cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu.
Tsarin biyan kudi na CIPS na samar da damar gudanar da hidimomin biyan kudi da cinikayya da kudin Sin RMB a ketare. A cewar Bankin Stanbic na Namibia, tsarin ka iya rage lokacin da ake dauka na kammala aikin biyan kudi da kimanin mintuna 35, haka kuma zai rage abun da ake kashewa na hada-hadar kudi tsakanin kasa da kasa, da rage dogaro kan wasu takardun kudi a tsakani.
Babban jami’in zartarwa na Bankin Standard a Namibia Erwin Tjipuka, ya ce bukatar ingantacciyar mafita ga hada-hadar biyan kudi tsakanin kasa da kasa na karuwa, bisa la’akari da matsayin Sin na daya daga cikin muhimman abokan cinikayyar Namibia.
shi kuwa jakadan kasar Sin a Namibia Zhao Weiping, maraba ya yi da kaddamar da tsarin a matsayin wani muhimmin mataki na zurfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu.
A cewar jakadan, kimanin kaso 17 na harkar biyan kudi daga Namibia zuwa ketare, na zuwa kasar Sin ne kai tsaye, inda yanzu haka ake yin kusan 1 bisa 3n wannan hada-hada da kudin RMB. Wannan ya nuna cewa tubalin amfani da RMB a hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Namibia na kara karfi. (Fa’iza Mustapha)














