Dakarun Shiyya 2 na ‘Operation FANSAN YAMMA’ sun kuɓutar da mutane 18 da aka yi garkuwa da su tare da kama wasu mutum biyu da ake zargin mambobin ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa ne, a wasu ayyukan yaƙi da ta’addanci daban-daban da suka gudanar a Jihar Zamfara.
An gudanar da ayyukan ne a ranar 10 ga Agusta, 2026, bayan samun bayanan sirri da suka shafi ayyukan ‘yan ta’adda da kuma kiran neman agaji daga wasu yankuna na jihar.
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji na Shiyya 2, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Gusau.
A cewarsa, a samamen farko, dakarun sun mayar da martani ga wani kiran gaggawa da ya shafi ganin wasu ‘yan ta’adda a wajen ƙauyen Sabon Gari, da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda.
Danja ya ce bayan isarsu yankin, dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan, inda suka samu nasarar kuɓutar da mutane 18 da aka yi garkuwa da su, ciki har da Alhaji Aminu Dayau da ‘ya’yansa.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere ta hayin wani kogi tare da wasu daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su, kafin dakarun su samu damar kuɓutar da su.














