Matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da cibiyar koyon fasahar zamani a garin Lafia, jihar Nasarawa, a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwuiwar hukumar ci gaban fasahar sadarwa ta ƙasa (NITDA).
Ta ce cibiyar na daga cikin cibiyoyi 10 da aka ƙaddamar a zagaye na farko, kuma ana ci gaba da gina wasu a sauran jihohi domin bunƙasa ilimin dijital.
- Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu
- Dubi Ga Rayuwar Uwargidan Shugaban Nijeriya, Oluremi Tinubu
A cewarta, manufar shirin ita ce samar da damar koyon fasahar zamani ga matasa domin su taka muhimmiyar rawa a ci gaban tattalin arzikin ƙasar. Ta yabawa NITDA bisa ƙoƙarinta wajen aiwatar da shirin, wanda ya haɗa da kafa cibiyoyi 296 na koyon dijital a faɗin Nijeriya.
Darakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa, ya bayyana cewa hukumar na shirin ƙara kafa 148 nan da ƙarshen shekara, domin kaiwa 586 kafin shekarar 2027. Ya ce shirin fasahar zamani na da muhimmanci wajen tallafa wa manufar gwamnatin Tinubu kawo sauyi da bunƙasa tattalin arziƙin zamani.
A nasa jawabin, Darakta Janar na hukumar fasahar sadarwa ta jihar Nasarawa, Sani Haruna Sani, ya ce cibiyar za ta mai da hankali kan horar da matasa a fannoni kamar tsaron yanar gizo da binciken laifukan da ake aikatawa a intanet. Ya ƙara da cewa za a horar da matasa 15 a kowane mako har zuwa Disamba 2026, tare da kira ga matasan jihar su yi amfani da damar wajen bunƙasa kansu da tattalin arziƙin ƙasa.












