A yau Jumma’a, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2025, an kafa sabbin kamfanoni na kasashen waje guda 24,018 a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna an samu karuwarsu da kashi 10.4 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
Daga watan Janairu zuwa Mayu, ainihin jimillar jarin waje na kai-tsaye, watau FDI da aka yi amfani da shi a masana’antun fasahohin kasar Sin ta kai yuan biliyan 109.04, inda jarin na FDI ya karu da kashi 146 cikin 100 a fannin hada-hadar kasuwanci ta shafin intanet, da kashi 74.9 cikin 100 a fannin kera kayayayakin jiragen sama, da kashi 59.2 bisa 100 a fannin samar da sinadaran harhada magunguna, da kuma karin kashi 20 cikin 100 a fannin kera na’urori da kayayyakin aikin likitanci. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp