An kaddamar da taron tattaunawa na masanan “Global South”, wato kasashe masu tasowa da na masu saurin ci gaba karo na biyu a jiya Alhamis a birnin Nanjing fadar mulkin lardin Jiangsu na kasar Sin, inda kamfanin CMG, da CASS, da jami’o’in Tsinghua, da Fudan da Renmin na kasar Sin, da sauran wasu jami’o’i 200 na kasar Sin da na ketare, suka kafa kawancen hadin gwiwar taron masanan “Global South”, a karkashin jagorancin ma’aikatar cudanya da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na JKS.
Makasudin kafa kawancen, shi ne tabbatar da muhimman shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, yayin taron tattaunawar shugabannin kasashen mambobin kungiyar “BRICS+”, wanda ya gudana a birnin Kazan na kasar Rasha, da kuma ingiza cudanyar al’adu, da dabarun tafiyar da harkokin kasa tsakanin kasashe daban daban.
Kazalika kawancen zai samar da wani tsarin raya huldar abokantaka tsakanin masanan kasashe masu tasowa da na masu saurin ci gaba. Haka kuma, zai samar da karin dabaru na gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen. (Mai fassara: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp