• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kama Bokan Da Ke Lalata Da Ya Da Kanwa A Ondo

by Sabo Ahmad
2 years ago
in Kotu Da Ɗansanda
0
An Kama Bokan Da Ke Lalata Da Ya Da Kanwa A Ondo
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

An kama wani boka da ke ci da sunan addini a wata cocin da ke Ajuwon ta jihar Ogun, Mista Joseph Ogundeji, da laifi hada ya da kanwa yana zina da su, har ya yi wa daya daga cikinsu ciki, wanda hakan ta sa ‘yansanda suka damke shi.

‘Yansanda sun kama Ogundeji da ke jihar Ogun sakamakon zargin da ake yi masa na yin lalata da ya da kanwa har ya yi wa daya daga cikinsu ciki.

  • Shugaba Xi Da Uwargidansa Sun Gana Da Sarki Da Sarauniyar Thailand
  • Yadda Mutuwar Abokai Biyu Ta Fallasa Lalacewar Asibitocin Jihar Neja

An kama wanda ake zargin ne sakamakon karar da uban yaran ya kai ofishin ‘yansanda da ke Ajuwon kan zargin yin lalata da ‘ya’yansa mata guda biyu.

Mahaifin yaran ya shaida wa ‘yansanda cewa, ya lura da cewa, daya daga cikin yaran nasa mai shekara 16 ta yi ciki.

Da ake yi masa tambayoyi kan wannan badala da ya yi, sai ya ce shi ma ba da son ransa ya yi hakan ba, sai dai kawai saboda an yi masa wahayi ne ya yi hakan.

Labarai Masu Nasaba

NDLEA Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 75 Da Laifin Safarar Muggan Kwayoyi

‘Yansanda Sun Kama Mutum 245 Da Miyagun Kwayoyi Da Makamai A Abuja

Jami’in hulda na rundunar ‘yansandan jihar Ogun,Abimbola Oyeyemi, ya ce, DPO da ke Ajuwon, SP Andrew Akinseye, ya ce, samun wannan rahoton ke da wuya, ‘yansanda suka damko wanda ake zargin domin gudanar da bincike. “A okacin gudanar da binciken wanda ake zargin ya amsa laifinsa” in ji Oyeyemi.

Lokacin gudanar da binciken an gano cewa, bokan yana lalata da wata karamar yarinya mai kimanin shekara 13, kanwar wadda ya yi yi wa cikin.

“’Yan matan guda biyu sun gaya wa ‘yansanda cewa, nayan an tashi daga coci bokan zai ce su same shi a gida, a nan ne kuma ya lalata su.

“Sun ci gaba da cewa,duk lokacin da suka zo gidan bokan,yakan ba su wani abu su ci. Da zarar sun ci sai bacci ya dauke su, sai sun tashi su ga alamun cewa, bokan ya yi zina da su,” kamar yadda Oyeyemi ta bayyana.

Da aka tambaye su ko mai ya sa ba su gaya wa iyayensu ba, sai Oyeyemi, ta ce, bokan ya ce, matukar suka gaya wa wani zai kashe su.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Lanne Bankole ya bayar da umarnin a mayar da wanda ake zargin sashin binciken manyan laifuka, don ci gaba da bincike.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AsiriBokaLalataOndo
ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Aikin Tono Man Fetur A Jihohin Bauchi Da Gombe

Next Post

‘Yan Bindiga Sun Harbe ‘Yan Sanda Uku A Shingen Bincike Da Ke Enugu

Related

Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Kamfanin LEADERSHIP Da NDLEA Sun Kulla Kawance
Kotu Da Ɗansanda

NDLEA Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 75 Da Laifin Safarar Muggan Kwayoyi

1 month ago
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum 245 Da Miyagun Kwayoyi Da Makamai A Abuja

2 months ago
‘Yansanda A Legas Sun Kama Mutum 35 Da Ake Zargi Da Fashi Cikin Mako Guda
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda A Legas Sun Kama Mutum 35 Da Ake Zargi Da Fashi Cikin Mako Guda

2 months ago
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Na Farautar Wadanda Suka Kashe Dalibi A Katsina

2 months ago
Rikita-rikitar Da Ta Biyo Bayan Mutuwar Mawaki Mohbad
Kotu Da Ɗansanda

MohBad: Nurse Za Ta Fuskanci Shari’a, Sannan Kotu Ta Wanke Naira Marley, Sam Larry Da PrimeBoy

2 months ago
‘Yansanda Sun Kubutar Da Wata Mata Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Otal Din Abuja
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kubutar Da Wata Mata Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Otal Din Abuja

3 months ago
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Harbe ‘Yan Sanda Uku A Shingen Bincike Da Ke Enugu

'Yan Bindiga Sun Harbe 'Yan Sanda Uku A Shingen Bincike Da Ke Enugu

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

May 14, 2025
Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

May 14, 2025
JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu

JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025

May 14, 2025
A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

May 14, 2025
Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

May 14, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

May 14, 2025
Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

May 14, 2025
Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha

Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha

May 14, 2025
Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.