Hukumomin Saudiyya sun kama wani dan Nijeriya daya da ‘yan Saudiyya uku bisa zargin safarar hodar ibilis da ta kai nauyin kilogiram 2.2 a kasar.
Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yansandan kasar ya ce ya samu nasarar dakile yunkurin shigar da hodar ibilis zuwa biranen Riyadh da Jeddah.
- Ina Kammala Wa’adin Mulkina Na Biyu Zan Yi Ritaya Daga Siyasa – Gwamna Sule
- Sauyin Gwamnati: Wainar Da Ake Toyawa A Jihohin Da ‘Yan Adawa Za Su Karbi Mulki
‘Yansandan sun ce mutanen hudu sun dade suna aikata laifin safarar hodar ibilis din tare da sayar da ita a cikin kasar ta hanyar amfani da wasu miyagun dabaru.
Jami’an ‘yansandan sun ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.
Safarar kwaya dai babban laifi ne a Saudiyya da za a iya yanke wa mutum hukuncin daurin shekaru masu yawa a gidan yari.