An kama mai shiga tsakanin Iyalai da masu garkuwar fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wanda aka kaima hari a Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022, Malam Tukur Mamu, a Masar.
Mamu wanda ke rike da sarautar gargajiya ta ‘Dan Iya’ a masarautar Fika a jihar Yobe, an kama shi ne a filin jirgin sama na Alkahira akan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya.
Mamu, shi ne mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna, ya fara tattaunawa da ‘yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna, wanda suka yi awon gaba da fasinjoji da dama, bayan fara tattaunawa da su, lamarin ya kai ga sako fasinjoji sama da 20.
Daga baya ya janye daga aikin tattaunawar, saboda barazana ga lafiyarsa. Sai dai Mamu ya zama hanyar sadarwa tsakanin ‘yan ta’adda da gwamnati, a wani bangaren kuma tsakanin ‘yan ta’addan da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su.
Mamu, ya tabbatar wa manema labarai a ranar Laraba ce wa: “Ina kan hanyata ta zuwa Madina, Kasar Saudiyya ne suka tare ni a filin jirgin sama na Alkahira bisa umarnin gwamnatin Nijeriya.
“Ba a sami wani abu a hannuna ba. Don haka na tabbata jami’an DSS ne suka tura umarnin daga filin jirgin saman Kano, ba ni da abin boyewa kuma kamar yadda na ce ba na jin tsoronsu (DSS).”