Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta yi karin haske game da kama Tukur Manu, wanda yake shiga tsakanin wajen yin sulhu don sakin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ‘yan bindiga suka sace.
DSS ta fitar da sanarwa ta hannun kakakinta, Peter Afunanya, cewar an kama Mamu a kasar Masar kuma yanzu haka yana hannunsu inda zai amsa tambayoyi.
- Matsalar Karancin Iskar Gas Na Addabar Turai Yayin Da Amurka Ke Kulla Makarkashiya
- Al’ummar Kasashen Turai Na Dandana Kudar Rikicin Rasha Da Ukraine
“Muna tabbatar da cewa Manu, ya shiga hannun jami’an tsaro a Masar a ranar 6 ga Satumba, 2022 yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya. Tun daga lokacin aka dawo da shi Najeriya, yau, 7 ga Satumba, 2022 kuma yana hannu don amsa tambayoyi.
“Wannan matakin ya biyo bayan bukatar da rundunar sojin Najeriya, da jami’an tsaro da kuma hukumar leken asiri suka yi na dawo da Manu gida domin amsa tambayoyi masu muhimmanci kan binciken da ake gudanarwa kan wasu al’amuran tsaro a sassan kasar nan.
“Muna sanar da jama’a cewa doka za ta yi aiki yadda ya dace.”
An wayi gari da labarin yadda jami’an tsaro suka kama Mamu akan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.
A baya ya sanar da cewar yana dab da daina yin sulhu da ‘yan bindigar da suka fasinjojin sakamakon hatsari da rayuwarsa ke ciki.