Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta kama wani matashi dan shekara 24 mai suna Muanaenye Chekwube Bictor, da laifin yaudarar abokinsa gami da yin garkuwa da shi a hannun ’yan kungiyarsa.
Wakilinmu ya gano cewa wanda ake zargin ya shirya yin garkuwa da shi kuma ya karbi kudin fansa a Dala kwatankwacin Naira miliyan 5.3 tare da ‘yan kungiyarsa kafin a sako wanda aka sace.
- APC: Ko Sadaukarwar Ganduje Za Ta Dakile Barazanar Jam’iyyun Adawa A Zaben 2027?
- Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi, ya ce jami’an ‘yansandan da ke shalkwatar Uli Dibisional sun cafke wanda ake zargin.
Ikenga ya ce wanda ake zargin wanda a halin yanzu yana ba ‘yansanda hadin kai ta hanyar bayar da bayanai don taimakawa wajen cafke wadanda ake zargin.
Sanarwar ta kara da cewa, “Jami’an ‘yansanda da ke shalkwatar ‘yansanda ta Uli a yammacin ranar 26 ga watan Yuni, 2025, sun fallasa tare da kama wani Muanaenye Chekwube Bictor, mai shekaru 24, kan zargin satar mutane.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp