Jami’an tsaro sun samu nasarar kama daya daga cikin wadanda ake zarginsu da kai hari kan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a Zuba, da ke yankin babban birnin tarayya Abuja.
Dubun wanda aka Kaman mai suna Yalo ta cika ne, lokacin da ‘yan sintiri suka mamaye shi lokacin da yake fito wa daga mota a tashar Dan-Kogi, da ke Zuba.
- Majalisa Ta Tabbatar Da Arase A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yansanda
- Ministan Harkokin Wajen Argentina: Sin Muhimmiyar Abokiyar Cinikayya Ce Ta Argentina
Daga cikin ‘yan sintirin da suka kama shi, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce, lokacin da ‘ya sintiri na kungiyar Miyetti Allah suka ga Yalo,nan da nan suka gaya wa ‘yan sintiri, wadanda su kuma suka kama shi.
Bayan yi masa binciken kwakwaf an kama shi da kudi naira dubu dari da uku da taba da kuma leta.
Bayan da ‘yan sintirin suka kama wanda ake zargin sun mika shi ga DPO na Zuba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp