Marubutan almarar kimiyya na kasar Sin sun samu karramawa a daren Asabar a bikin ba da lambobin yabo na Hugo na bana.
Hai Ya, ya karbi lambar yabo ta mafi kyawun littafi mai suna “The Space-Time Painter” yayin da fitaccen mai zane-zane na kwamfuta Zhao Enzhe ya lashe kyautar mafi kyawun kwararren mai zane-zane.
- An Yi Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Mutane Masu Bukata Ta Musamman Ta Asiya A Hangzhou
- “Hanyar Siliki Ta Dijital” Na Ingiza Zamanantar Da Duniya
An bayyana sakamakon ne a bikin babban taron marubutan almarar kimiyya na duniya karo na 81 wanda aka fara daga ranar 18 zuwa 22 ga watan Oktoba a Chengdu, babban birnin lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin.
Baya ga wadanda suka yi nasara, akwai wasu fannoni da dama a bikin Hugo na bana, wadanda marubuta da masu zane-zane na kasar Sin suka samu lambobin yabo.
Lambar yabo ta Hugo, wacce aka fara gabatarwa a shekarar 1953 kuma ake gabatarwa kowace shekara tun 1955, lambar yabo ce ta almarar kimiyya. Mambobin kungiyar marubutan almarar Kimiyya na Duniya ne ke zaben wadanda ke samun Lambar yabo ta Hugo, kuma sune ke da alhakin bayar da shi. (Yahaya)