An Kammala Tantance Jaruman Shirin Birnin Dala

Shirin Birnin Dala

Daga Saddik Muhammad

A ranar Alhamis 15//7/2021 ne aka gudanar da taron tantance jaruman da za su fito a cikin shiri mai dogon Zango mai suna Birnin Dala.

Shirin wanda kamfanin Kumbo zai dauki nauyin shirya shi kuma nan da dan wani lokaci za a shiga aikin na sa, don haka aka yi taron tantance jaruman da za taka rawa a cikin sa.

A kalla jarumai kusan dari uku ne suka halarci wajen tantancewar da aka gudanar a dakin taro na Darru tauhid da ke kan titin Zaria a cikin garin Kano.

A lokacin da mu ke jin ta bakin Shugaban shirin na Birnin Dala, Ghali Abdullah wanda aka fi sani da Ghali Deezat dangane da wannan taron tantancewa da suka shirya.Ya bayyana mana cewar “Kamar yadda aka sani shi wannan shiri na Birnin Dala, shiri ne wanda aka fara gudanar da shi a matsayin wasan Kwaikwayo na rediyo a tashar Dala F M wanda aka shafe kusan shekaru biyu da rabi ana gudanar da shi, to bayan an kai wata gaba sai shirin ya tsaya, kuma daga lokacin da aka fara shi sai ya zama shirin ya dauki hankalin mutane, saboda irin yadda aka tabo abubuwa na al’ada ta Masarauta. Kuma abin da mu ke yi duk muna yi ne, domin dabbaka harshen Hausa da kuma al’adun Malam Bahaushe, wannan ta sa daga bangaren Masarautu da kuma manyan mutane, suna bibiyar mu har ma da yara masu karancin shekaru suna bibiya don su ji abin da ya faru na Sarauta a shekarun da suka shude, to Amma dai manufar wannan taron da muka yi a wannan lokaci shi ne domin mu tantance wadanda za su fito a matsayin jaruman shirin Birnin Dala, kuma duk da cewar akwai jarumai yan Kannywood, amma akwai bukatar a wannan fim din a kawo sababbin fuska saboda fim ne mai dogon Zango, domin idan ka dakko wanda aka san fuskar sa, idan ba ka yi wasa ba kana cikin aikin wani uzirin sa zai zo ba mamaki sai aikin ka ya kare, don haka muka ga lallai ya kamata mu yi taro mu kira mutane, domin su zo a gwada a tantance har a samar da wadanda suka dace su fito a matsayin jaruman fim din “.

Dangane da lokacin da a ke sa ran za a fara aikin da kuma wajen da za a yi aikin kuwa cewa ya yi” To da zarar mun kammala tantancewa za mu zauna da Daraktan mu fitar da lokacin da ya dace mu fara aikin. Muka wajen da za mu yi aikin, saboda alakar mu da Masarautu, tun a lokacin baya mun samu waje a Masarautar Rano wadda wajen ya fi dacewa da yanayin labarin mu, don haka a can mu ke sa ran za mu gudanar da aikin. ”

Ko me ya bambanta wannan fim din da sauran finafinan da a ke yi na sarautar Gargajiya?

To gaskiya abin da ya Bambanta su shi ne su wadanda aka saba gani sun takaita labarin ne kawai a iya zaman fada, amma mu mun fadada abin da wasu abubuwan da Sarki ya ke gusarwa a cikin gidan sa da kuma yadda ya ke yin Mu’amala da sauran Jama’a don haka akwai bambanci sosai, domin mu mun dauki abin ba da sunan wasa ba, a a yadda tsarin Sarauta ya ke to a haka za mu gudanar da aikin mu, kuma duk wanda ya ke bin shirin a lokacin da a ke gabatar da shi a Rediyon Dala to ya san abubuwan da mu ke gudanarwa wadanda su ke faruwa ne a zahiri ga sarakunan mu a cikin tsarin sarautar su. ”

Daga karshe Ghali Abdullah ya yi godiya ga dukkan jama’ar da su a halarci wajen da kuma wadanda suka bayar da gudummawa wajen shirya taron wanda aka samu aka yi shi cikin nasara.

Exit mobile version