A yau Juma’a, aka kammala taron dandalin Boao na kasashen Asiya na 2024, a birnin Boao dake lardin Hainan na kasar Sin, inda aka cimma matsaya kan jerin batutuwa.
Sakatare janar na dandalin Li Baodong, ya ce dukkan bangarori na sane da kalubalen da duniya ke fuskanta yanzu haka, yana mai cewa dukkan kasashe na fuskantar kalubale iri daya, ciki har da rashin kuzarin farfadowar tattalin arziki da karuwar rikice-rikice a yankuna. A cewarsa, ta hanyar hada hannu da aiki tare ne kadai za a iya shawo kan tarin kalubalen.
- Ana Sa Ran Dandalin Boao Na Bana Zai Hallara Mutane Kimanin 2,000
- Ministan Lafiya Na Yunkurin Samar Da Sabon Shirin Taskace Bayanan Majinyata
Ya kara da cewa, kasar Sin na kara samun ci gaba mai inganci da kara bude kofarta, kuma ana sa ran za ta ci gaba da zama mafi bayar da gudunmuwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
Cikin matsayar da aka cimma, an bayyana muhimmancin kirkire-kirkire a mastayin muhimmin karfi dake ingiza ci gaba, kuma ya kamata kasashe a fadin duniya su gaggauta daukar mataki kan matsalar sauyin yanayi.
Taron na bana ya gudana ne daga 26 zuwa 29 ga wata, bisa taken “Asiya da Duniya: Kalubale na Bai Daya, Nauye-Nauyen Kowa da Kowa.” (Fa’iza Mustapha)