Cibiyar ba da lambar yabo ta kasa ta bai wa kwamishinan ma’aikatar ayyuka da sufuri da gidaje na Jihar Katsina, Injiniya. Dr. Sani Magaji Ingawa lambar yabo a matsayin kwamishinan mafi kwazo a Nijeriya.
An karrama kwamishinan ne tare da gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar dokokin jihohi da kuma kwamishinoni a lokacin wani biki da ya gudana a ‘Merit House’ da ke Maitama a Abuja.
- Ƙaramin Ministan Mai Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Cibiyar Lantarki A Maiduguri
- Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Karramawar Da Sojoji Suka Yi Wa Seyi Tinubu
Babban sakataren ma’aikatar ayyuka da gidaje da sufuri na Jihar Katsina, Umar Isma’il Rigoji ne ya wakilci kwamishinan a lokacin bikin karramawar.
A lokacin bikin, shugaban cibiyar ba da lambar yabon ta kasa, Cif Perry Opara ya bayyana sadaukarwar kwamishinan a bangaren ayyuka, musamman abin da ya shafi duba ayyukan da gwamnan Katsina ke aiwatarwa karkashin ma’aikatar.
A wani labarin kuma. Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya ba da tabbacin cewa za a kaddamar da aikin tagwayen hanyar wajen gari da ta kewaye da ke garin Katsina a tsakiyar shekara 2025.
Gwamna Radda ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da yake duba aikin hanyar.
Gwamnan ya fahimci cewa, kamfanin da ke gudanar da aikin hanyar ya kai matakin a yaba masa, duba da yadda aikin ke gudana.