Sakamakon wani harin kwanton bauna da ‘yan bindiga suka yi wa gamayyar Jami’an tsaro, 10 sun rasu a dajin Anka na jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an tsaron ke dawo daga farmakin da suka kai a dajin Sunƙe, wanda aka samu nasarar kashe da dama daga cikin ‘yan bindigar tare da ƙwato makamai masu tarin yawa.
- Hajiya Safara’u, Mahaifiyar Gwamna Raɗɗa Ta Rasu
- Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027
A lokacin kwantan ɓaunar da aka yi musu a Bagega, an rasa rayukan Askarawa shida da ‘yan sa-kai huɗu. Har yanzu, akwai mutane uku da ba a gani ba wanda suka hada da biyu daga cikin Askarawa da ɗaya ɗan sa-kai.
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana alhini tare da yin addu’a ga waɗanda suka rasu, tana fatan samun zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da ƙasar baki-ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp