An yi wa wani matashi dukan kawo wuka har ya mutu saboda zarginsa da yin batanci ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (SAW) a Jihar Bauchi.
Rundunar ‘yansndan Jihar Bauchi, ta tabbatar da cewa matashin ya mutu ne, bayan da wasu matasa suka yi masa dukan da ya yi ajalinsa ranar Laraba.
- Rikicin Sarautar Kano: Kwankwaso Ya Caccaki Gwamnatin Tarayya, APC Ta Mayar Da Martani
- Rashin Wadatar Kayan Aiki: Yadda Nijeriya Ta Kasa Dakatar Da Asarar Naira Tiriliyan 1.4 A Sashen Kiwon Lafiya
Lamarin ya faru a yankin Nasaru da ke Karamar Hukumar Ningi ta jihar bisa zarginsa da aikata sabo da yin kalaman batanci ga Fiyayyen Halitta (SAW).
Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya sanar cewa rundunar ta yi matukar bakin ciki faruwar lamarin a kauyen Nasaru a ranar 19 ga watan Yuni, 2024.
“An shaida mana cewa wani mutum mai suna Usmanu suna muhawara game da wani sabon abu na Addini da aka sani da kungiyar ’yan Faira suke yi.
“Abin takaici, wannan ya haifar da tashin hankali da hatsaniya, wanda ya yi sanadiyyar rasa ransa,” in ji shi.
Wakil, ya ce kwamishinan ’yansanda, Auwal Musa Muhammad, ya yi Allah-wadai da abin da ya faru tare da jaddada muhimmancin bin doka da oda.
Ya bayyana kudirin rundunar na kara kaimi wajen sa ido domin tabbatar da tsaro ga dukkan mazauna yankin.
Ya shawarci jama’a da su yi aiki kafada da kafada da hukumomi domin tabbatar da doka da oda, kuma su guji daukar doka a hannunsu.
Ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da fargaba ba, domin an samu zaman lafiya a yankin da lamarin ya shafa.
Rahotanni sun ce an kashe wanda ake zargin ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Laraba bayan wata takaddama kan wata kungiyar addini.
Lamarin dai ya ja hankalin mutane da dama da ke kusa da wurin inda suka rika bin muhawara a tsakaninsu.