Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello, ya ce dakarun sojin Nijeriya sun dakile wani hari da wasu ‘yan tada kayar baya suka kai a wani sansanin soji da ke yankin Sarkin Pawa a jihar.
A cewar NAN, an tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar yada labaran gwamnan, Mary Noel-Berje, ta fitar a ranar Litinin.
- Ambaliyar Ruwa Ta Ci Rayukan Mutum 4 Tare Da Mamaye Kauyuka 11 A Yobe
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Yi Rashin Nasara A Hannun Morocco
Bello ya ce maharan sun yi yunkurin kai hari a garin da sansanin sojoji da misalin karfe 2:23 na safiyar ranar Litinin.
Ya ce sojojin da suka amsa kiran gaggawa sun isa garin Sarkin Pawa cikin mintuna 30, kuma an kashe da yawa daga cikin maharan a wani artabu da suka yi.
“Harin da aka shirya zai yi muni idan ba don gaggawar mayar da martani daga jiga-jigan sojojin da ke Sarkin-Pawa da kuma tawagar da suka yi gaggawar amsa kiran gaggawa ba,” in ji shi.
“Ba a samu asarar rayuka a bangaren sojoji ba yayin da aka ce an kashe ‘yan ta’adda da dama yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
“Amsa kiran gaggawar da sojojin da ke Munya suka yi da kuma martanin da rundunar ta bayar game da kiran da suka yi daga Minna abin yabawa ne.”
Ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na shawo kan lamarin.
“Gwamnatin jihar Neja ta amince da kokarin sojoji da sauran jami’an tsaro wajen yaki da rashin tsaro a jihar,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar wa da mazauna jihar cewa jihar na hada hannu da gwamnatin tarayya domin ganin an kawar da masu aikata laifukan da ke kai hare-hare a yankunan manoma da daidaita rayuwar al’umma.