Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar mutane uku da kuma jikkatar wasu bakwai sakamakon rikici da ya ɓarke a ƙaramar hukumar Birniwa.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Lawan Shiisu Adam, ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai hari garin Dagaceri.
- Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3
Maharan sun ƙone gidaje da dama tare da kai wa mazauna garin hari.
Shiisu, ya ce jami’an tsaro sun isa wajen da abin ya faru cikin gaggawa, su tabbatar da zaman lafiya, sannan suka kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun samu wayoyin salula da kayan tsafi a wajen da aka kai harin.
SP Shiisu ya ce bincike na ci gaba domin gano musabbabin ɓarkewar rikicin.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ƙara haɗa kai da jami’an tsaro da kuma gaggawar bayar da rahoto idan suka lura da wani abin da zai iya janyo rikici, domin kauce wa zubar da jini.













