Wata kungiyar matasa a Dokan Daji da ke kudancin Kaduna, ta yi kira ga sojoji da su kare al’ummominsu daga hare-haren ‘yan bindiga da ke ci gaba da addabarsu.
Shugaban kungiyar, Aminu Khalid, ya ce sama da mutum 50 aka kashe, kuma an sace sama da mutum 170 tun daga watan Afrilun 2024.
- Dan Nijeriya Lookman Na Kan Gaba Wajen Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika Ta Bana
- Gwamna Lawal Ya Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 14
Iyalan mazauna yankin sun biya sama da Naira miliyan 700 a matsayin kudin fansa, yayin da wasu daga cikin wadanda aka sace har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.
Khalid, ya koka cewa al’ummar Dokan Karji da ke karamar hukumar Kauru, da ke da zaman lafiya a baya, yanzu ta zama wajen tashin hankali.
Mafi yawan mazauna yankin sun tsere daga gidajensu saboda hare-haren mahara.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da su tura dakarun soji don dakile kisan jama’a, garkuwa da mutane, da korar mazauna yankin daga gidajensu.
Khalid, ya yaba wa kokarin Kwamandan Runduna ta 7 wajen yakar ‘yan bindiga.
Amma ya jaddada cewa akwai bukatar karin taimakon sojoji don ceto al’ummarsu daga wannan tashin hankali.