A wani gagarumin farmakin da sojoji suka kai, fitaccen shugaban ‘yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma, Bello Turji, ya tsere daga sansaninsa zuwa karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara bayan kashe da dama daga cikin sauran shugabannin ‘yan bindiga a jihar.
An kuma rahoto cewa, sojojin sun yi nasarar kashe babban mataimakin Turji a shugabanci, Aminu Kanawa, a wani hari da suka kai dajin Fakai.
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Inganta Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa A Taron Davos
- Borrusia Dortmund Ta Sallami Kocinta, Nuri Sahin
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Kanawa ya yi kaurin suna wajen kitsa wasu munanan hare-haren ta’addanci a wasu yankuna da suka hada da kananan hukumomin Zurmi, Shinkafi, Isa, da Sabon Birni a jihohin Zamfara da Sakkwato. Kawar da shi, babbar nasara ce ga sojoji kuma rauni ne ga mayakan Turji.
Baya ga Kanawa, sojojin sun kuma kashe wasu manyan mayakan Turji da suka hada da Dosso, Dan’uwan Turji, da kuma Danbokolo.
A wani gagarumin artabu da aka yi a Gebe, da ke karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto, sojoji sun yi nasarar harbe wasu ‘yan bindiga da ke kokarin tserewa. Daga cikin wadanda aka kashe akwai wasu manyan kwamandoji: Abu Dan Shehu, Jabbi Dogo, Dan Kane, Basiru Yellow, Kabiru Gebe, Bello Buba, da Dan Inna, wanda aka fi sani da ‘Kahon-Saniya-yafi-Bahaushe’.
Bayanan sirri da aka samu a yankin sun nuna cewa, an ga mayakan Turji a kan babura, suna jigilar ‘yan uwansu da suka samu raunuka ta hanyar yankunan Galadi, Damaga, Rudunu, da Danbenchi sun nufi Garsa/Kadanya zuwa yankin Bayan Ruwa.