An yi wa wani jami’in soja kwanton bauna tare da wasu mutanen 24 mazauna kananan hukumomin Ussa da Takum a Jihar Taraba.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba, Abdullahi Usman, mutane 24 ne suka mutu.
- Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da Ukraine Ta Nuna Yadda Sin Ta Sauke Nauyi Dake Wuyanta
- Da Dumi-Dumi: NEC Ta Dakatar Da Cire Tallafin Man Fetur
“Jami’in sojan da ya fito daga shingen binciken da ke dawowa barikin bataliya ta 93 an yi masa kwanton bauna aka kashe shi, duk da cewa ba a kwace masa babur dinsa ba, kuma aka yi sa’a ba shi da bindiga a tare da shi.
“Wadanda ba a san ko su wane ne ba ne suka kashe shi, kuma an fara bincike don bankado wadanda suka aikata kisan. Bisa kididdigar da aka yi, an kashe ‘yan asalin kabilar Kuteb 20 yayin da wasu Fulani makiyaya uku kuma suka mutu a sakamakon rikicin,” in ji kakakin.
Ya kara da cewa babbar matsalar da ta dakile dawo da zaman lafiya a yankin, ita ce ikirarin da Fulani makiyaya suka yi na cewa manoman Kuteb sun yi garkuwa da shanunsu da kuma hana wasu bangarorin da suka kasa shiga gonakinsu saboda fargabar da ake yi musu.
“Matsalar da muke fuskanta a halin yanzu ita ce, Fulani na ikirarin cewa an sace musu shanu kuma ana garkuwa da su a yankunan manoman Kuteb yayin da ‘yan Kuteb ke fargabar zuwa gona saboda fargabar harin Fulani makiyaya.
“Kwamishanan ‘yan sanda ya yi kira ga shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da ke Ussa da su yi kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin,” in ji shi.
Shugaban kungiyar Kuteb Yatgso ta Nijeriya, Emmanuel Ukwen, ya ce a matsayinsa na shugaban al’ummarsa bai ga gwamnatin jihar ta ziyarci mutanensa ba ko ta tausaya musu ba.
Sannan ya musanta sama wa jama’arsa matsuguni sakamakon rikicin da ya yi sanadin raba wasu da muhallansu.