Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce, jami’anta sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga guda hudu (4) a musayar wuta da suka yi da su da kama wata mata da take musu safarar bindigogi da alburusai a jihar Kaduna.
Kamar yadda jami’in hulda da jama’a na hukumar reshen jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige, ya shaida ta cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Mutan 3 Yankan Rago Da Sace Wasu Da Dama A Wani Sabon Hari A Neja
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutun 3, Sun Sace 30 A Jihar Neja
Jalige ya ce, nasarar ta biyo bayan kokarin jami’an ‘yan sanda na STS da hadin guiwar sojojin Operation Yaki suka samu wurin kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga, inda a ranar 15 ga watan Yuni suka cafke wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne a kan hanyar Saminaka zuwa Jos.
Ya ce, an kama ‘yan bindigan ne a cikin wata mota kirar Sharon mai launin bulu tare da matukinta mai suna James Dawi Dan shekara 31 a duniya mazaunin yankin Vom da ke Kudancin jihar Filato.
Ya kara da cewa a wannan yanayin da suka tabbatar ba za su iya tsallake tarkon jami’an tsaron ba gami da kokarinsu na kai bindigogi ga abokan cin burminsu, nan take suka bude ruwan harsasai ga jami’an tsaron.
Jami’in yada labaran ya ci gaba da cewa, cikin dabarun na aiki da kwarewa, jami’an tsaron sun samu nasarar harbin hudu daga cikin ‘yan bindigan kana an kwashesu zuwa asibitin koyarwa ta Barau Dikko da ke Kaduna inda likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Ya ce, sun samu nasarar kwato wasu makamai daga wajen ‘yan bindigan bayan da aka sha karfinsu, “A yayin artabun an kama wata mace da ake bincikenta ta tabbatar da kanta cewa tana safaran bindigogi da alburusai ga ‘yan bindiga a yankin Kaduna.”
Ya ce, bincike dai na cigaba da gudana domin dakile aniyar bata-garin da suka addabi Kaduna da garkuwa da mutane da fashi da makami.