Dakarun da ke aiki da rundunar ‘Operation SAFE HAVEN’ (OPSH) sun kashe ‘yan bindiga hudu tare da cafke akalla mutum 19 da ake zargi da suka hada da masu garkuwa da mutum da barayin shanu da kuma ‘yan fashi da makami a wani samame da suka kai maboyar ‘yan ta’adda a Jihohin Filato da Kaduna.
Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter (D).
“An kama mutum 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban. An kama uku da laifin yin garkuwa da wani mutum yayin da aka kama hudu da laifin kisan kai.
An kama mutum hudu da ake zargi da kai hare-hare a kauyuka, biyu kuma da laifin safarar miyagun kwayoyi, yayin da aka kashe ‘yan bindiga hudu. Har ila yau, an kubutar da mutum hudu daga hannun masu garkuwa, yayin da aka dakile hare-hare shida kan al’ummomin da ba su da karfi, sannan an amsa kiran gaggawa 13,” in ji sanarwar a wani bangare.
A ranar 29 ga Oktoba, 2023, sojojin sun kama wasu da ake zargin dillalan miyagun kwayoyi ne, Mista Obinna Nwafor da Fatai Lawal a Kasuwar Kujiya Bukuru a Karamar Hukumar Jos ta Kudu, Jihar Filato, inda suka kwato wata bindiga kirar gida.
Washegari jami’an OPSH na Sector 7 sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, Bawa Ahmad a Kauyen Kamuru da ke Karamar Hukumar Zango Kataf a Jihar Kaduna tare da kwato bindiga guda daya ta gida da kuma harsashi.
“A ranar 30 ga Oktoba, 2023, bisa ga sahihin labari, sojoji sun kama wasu mutum uku, Ibrahim Mohammed, Salisu Abdullahi da Idris Abdullahi da hada baki a harin da aka kai wa manoma a Kauyen Mai Hakorin Gold da ke Karamar Hukumar Bokkos, Jihar Filato.
“Hakazalika, sojoji sun kama wasu mutum uku, Dabid Emmanuel, Moses Dalyop da Gabriel Dabou, da hadin baki a kisan wani direban babur mai suna Abdulkarim Saidu, a Kauyen Shonong dake Karamar Hukumar Riyom, Jihar Filato.
“An kama wadanda ake zargin ne a kauyen Fang da ke Karamar Hukumar Riyom a ranar 30 ga Oktoba 2023. Wadanda ake zargin sun jagoranci sojoji wajen nemo gawar direban babur da aka kashe. A wannan rana, sojoji sun ceto wata Mis Abigail Felid da aka yi garkuwa da su a ranar 28 ga Oktoba, 2023, a Kauyen Angwan Malam da ke Karamar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna. Tuni dai matar da aka yi garkuwar da ita aka sake hada ta da danginta,” in ji sanarwar.
A ranar 1 ga Nuwamba, an kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar babura Samaila Nasiru, Bashir Sani a babban yankin Riyom na Jihar Filato. Sojojin tare da hadin gwiwar Cibilian Joint Task Force sun kuma ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a unguwar Zobolo da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.