Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa an kashe ‘yan ta’adda 6,260 a fadin kasar ta hanyar aikin hadin gwiwa na sojojin kasar a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin suka kuma kwato danyen mai da wanda aka sarrafa da aka kiyasta darajarsa ta kai sama da Naira biliyan 83 a cikin wannan lokaci.
- Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
- Masarautar Gaya Ta Ƙwace Sarautar Wazirin Gaya Da Ta Bai Wa Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano
Mataimakin Darakta mai kula da harkokin yada labarai na tsaro, Brig.-Gen. Ibrahim Abu-Mawashi ya bayyana hakan a lokacin da yake bayani kan nasarorin da sojojin suka samu a cikin shekaru biyu a wani taro na manema labarai a hedikwatar tsaro, ranar Alhamis.
Brig.-Gen. Abu-Mawashi ya kara da cewa an kama ‘yan ta’adda 14,138 da sauran masu aikata laifuka yayin da aka ceto mutane 5,365 a cikin wannan lokaci.
Abu-Mawashi ya ci gaba da cewa, sojojin sun kwato daruruwan makamai da kuma harsashi da yawa duk acikin wannan lokaci.