Rundunar Sojan Sama ta Rundunar hadin gwiwa ta Operation Fasin Yamma (OPFY) ta tabbatar da kashe ‘yan ta’adda sama da 30 a jihar Zamfara a wani harin da ta kai ta sama a ranar 4 ga Agusta, 2025.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar OPFY, Kaftin David Adewusi ya fitar a ranar Alhamis, ya ce, an kai harin ne a wani gagarumin taro na ‘yan ta’adda a gindin tsaunin Asola da ke unguwar Yankuzo a karamar hukumar Tsafe, inda suka hallara domin daurin aure.
- Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin
- Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?
Sanarwar ta kara da cewa, “Harin, wanda aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri, an kai shi ne ga ‘yan ta’adda dake yankin Faskari da Kankara a jihar Katsina, da kuma wasu sassa na Zamfara.
“An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi
Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna kan hanyar zuwa kauyen Yankuzo, inda rahotanni suka ce an kai ‘yan ta’addan da suka jikkata domin yi musu magani.
A cewar majiyoyi da bayanan sirri daga Kauyen, an kashe ‘yan ta’adda fiye da 30 a yayin samamen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp