Wani mai magana da yawun rundunar tsaron gabar teku ta kasar Sin (CCG) ya bayyana cewa, an yi gargadi tare da korar wani jirgin kamun kifi na kasar Japan a yau Talata, bayan da ya shiga yankin ruwa na Diaoyu Dao na kasar Sin ba bisa ka’ida ba.
Mai magana da yawun rundunar ta CCG Liu Dejun, ya kara da cewa rundunar ta dauki matakan da suka dace ne daidai da doka, inda ta yi gargadi tare da korar jirgin.
Yayin da yake jaddada cewa, Diaoyu Dao da tsibiran da ke da alaka da shi, yanki ne na gado na kasar Sin, Liu ya bukaci kasar Japan da ta gaggauta dakatar da duk wasu ayyuka na keta iyaka da tsokana a cikin yankunan ruwan.
Jami’in ya kara da cewa, “CCG za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tabbatar da doka da oda a yankin ruwan Diaoyu Dao don tabbatar da cikakken kare ‘yancin yankunan kasar Sin da hakkoki da kuma muradunta na teku.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














