Jam’iyyar APC a mazabar Galadima da ke karamar hukumar Gusau jihar Zamfara, ta kori shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Danfulani Maikatako, daga jam’iyyar, inda ta ce ba shi da ikon jagorantar jam’iyyar a jihar.
Jamiyyar ta babbar da haka ne a taron manema labarai da ta yi yau Asabar a Gusau, babban birnin jihar.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 30 Da Wani Malami A Zamfara
- Gwamnan Zamfara Ya Sauke Nauyin Bashin Haƙƙoƙin Ma’aikata Na Fiye Da Naira Biliyan 4
’Yan majalisar zartarwar jam’iyyar APC na mazabar Galadima sun kuduri aniyar ceto jam’iyyar daga mummunan shugabanci na shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Tukur Danfulani.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Galadima a Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Garba Bello, ya bayyana cewa shugabani 16 daga cikin 27 na yankin sun sanya hannu kan korar Tukur Danfulani daga jam’iyyar.
A cewarsa, kashi 90 cikin 100 na mambobin jam’iyyar APC a mazabar Galadima ta Karaman Hukumar Gusau sun amince baki daya tare da sanar da ‘ya’yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Gusau da hedikwatar jiha da ta kasa cewa sun kori Tukur Danfulani Maikatako daga jam’iyyar.