An Kubutar Da Mutum 6 Cikin Wadanda Aka Sace Yayin Harin Tashar Jirgin Kasa A Jihar Edo
Gwamnatin jihar Edo ta ce, an ceto mutane shida cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a yayin harin da aka kai a tashar jirgin kasa a jihar.
- An Tabbatar Da Bacewar Fasinjoji 31 Bayan Kai Hari Kan Jirgin Kasa A Jihar Edo
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Tashar Jirgin Kasa, Sun Yi Garkuwa Da Fasinjoji Da Dama A Edo
Gwamnatin jihar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
Wadanda aka ceto sun hada da dattijo mai shekaru 65 da wata mace mai shayarwa da jaririnta da yarinya ‘yar shekara shida da kuma wasu ‘yan gida daya su biyu masu shekaru 2 da 5.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp