Yau Jumma’a da safe ne aka bude taron kolin kasar Sin da kasashen Tsakiyar Asiya karo na 1 a birnin Xi’an, babban birnin lardin Shaanxi da ke tsakiyar kasar Sin, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jagoranci taron, tare da gabatar da jawabi.
A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya gabatar da ra’ayinsa kan yadda za a raya yankin tsakiyar Asiya, inda ya ce, tilas ne a kiyaye ikon mulki da tsaro, da ‘yanci da cikakkun yankunan kasashen yankin tsakiyar Asiya, kana a girmama hanyar da al’ummomin kasashen suka zaba da kansu wajen raya kasashensu, a goyi bayan kokarin yankin na tsakiyar Asiya na samun zaman lafiya, jituwa da kwanciyar hankali. Sa’an nan kuma, babu wanda ya isa ya tada rashin jituwa, da kuma adawa da juna a yankin tsakiyar Asiya, kana bai kamata a nemi samun ribar siyasa a yankin ba.
Dangane da gina al’ummomin Sin da tsakiyar Asiya mai makoma ta bai daya, Xi ya nuna cewa, wajibi ne bangarorin 2 su tsaya tsayin daga kan mara wa juna baya sosai a wasu muhimman al’amuran da suka shafi ikon mulkin kasa, ‘yancin kai, mutuncin al’umma, bunkasuwa cikin dogon lokaci da dai sauransu. Kana kuma wajibi ne su nemi samun bunkasuwa tare, su ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Har ila yau wajibi ne su tabbatar da tsaro dake shafar kowa, su nuna adawa da masu neman tsoma baki cikin harkokin cikin gidansu, da yunkurin yin juyin mulki, su kiyaye yaki da ‘yan a-ware, ‘yan ta’adda da masu tsattauran ra’ayi. Baya ga haka kuma, bangarorin 2 za su kiyaye dankon zumunci a tsakaninsu a nan gaba, da zurfafa yin koyi da juna ta fuskar wayewar kai.
Ban da haka kuma, shugaban na kasar Sin ya gabatar da shawarwari guda 8 kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya, wato kara kafa tsare-tsare, kyautata huldar tattalin arziki da ciniki, zurfafa hadewar juna, kara yin hadin gwiwa ta fuskar makamashi, kara azama kan yin kirkire-kirkire maras gurbata muhalli, inganta karfin bunkasuwa, kara yin tattaunawa ta fannin wayewar kai, da kiyaye zaman lafiya a yankin.
Kana shugabannin Sin da kasashe 5 na tsakiyar Asiya sun amince da kafa tsarin taron shugabannin kasashen, wanda za a shirya a kasar Sin da kasashen tsakiyar Asiya daya bayan daya a ko wadanne shekaru 2. Za a gudanar da taron kolin a kasar Kazakhstan a shekarar 2025. Haka kuma shugabannin sun amince da kafa ofishin sakatariya mai kula da tsarin kasar Sin da kasashen tsakiyar Asiya.
Bugu da kari, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugabannin kasashen tsakiyar Asiya guda 5, sun sanya hannu kan “Sanarwar Xi’an”, tare da amincewa da jerin sakamakon da aka cimma a yayin taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya.
A Juma’a ne, aka kammala taron kwanaki biyu a birnin Xi’an na lardin Shaanxi dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin. (Tasallah Yuan, Ibrahim Yaya)