An kwantar da tsohon shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir a wani asibiti sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita.
al-Bashir wanda ya shafe shekaru 30 yana mulki kafin a hambarar da shi a wani bore da al’ummar kasar suka yi a 2019.
- Sake Dawo Da Sanusi II Sarautar Kano Ya Fi Min Komai Dadi – El-RufaiÂ
- Majalisa Ta Tabbatar Da Nadin Kudirat A Matsayin Alkalin Alkalan Nijeriya
Bayan hambarar da shi, shugabannin sojojin kasar sun daure shi a gidan yari.
Lauyansa ya bayyana cewa an dauke al-Bashir mai shekaru 80 a duniya daga wani sansanin soji da ke wajen babban birnin kasar Sudan, Khartoum, a ranar Talata.
Lauyan ya kara da cewa lafiyar al-Bashir ta tabarbare a baya-bayan nan, amma yanayin bai tsananta ba.
Haka kuma tsohon ministan tsaron Sudan Abdel-Rahim Muhammad Husseien ya koma arewacin kasar.
An kama shi ne jim kadan bayan hambarar da al-Bashir a shekara 2019.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dai tana neman mutanen biyu kan tuhumar laifukan yaki da kisan kare dangi.