An kwashe wasu dabbobin jeji da suka haɗa da maciji, kada da ɗan giwa daga gidan tsohon Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, zuwa Gidan Zoo na Kano, bayan da wani maciji ya tsere daga gidan nasa ya tayar da hankula a unguwar Daneji da kewaye.
Daraktan gudanarwa na Gidan Zoo na Kano, Sadik Muhammad Kura, ya tabbatar da hakan a wani shiri na rediyo da aka yi a ranar Lahadi. Ya ce an cafke macijin cikin ƙoshin lafiya tare da kada da ɗan Giwa da aka same su a gidan.
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya
- Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)
“Shi kansa tsohon Akanta-Janar ɗin ne ya miƙa dabbobin, bayan da mazauna unguwar suka nuna fargaba,” in ji Muhammad, yana mai tabbatarwa da jama’a cewa yanzu haka dabbobin suna hannun hukuma cikin tsaro a gidan zoo.
Ya ƙara da cewa, Ahmed Idris yana da lasisin mallakar irin waɗannan dabbobi, wanda dokar mallakar dabbobin jeji ta amince da shi idan mutum ya cika sharuddan kiwo da kare lafiyar jama’a.
Muhammad ya ce duk da cewa ɗan Giwa ne, dokar na buƙatar sabunta lasisi a duk shekara tare da kwashe dabbobin zuwa gidan zoo idan sun fara girma. Ya kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp