Wani tsoho mai suna Uchelue Ikechukwu mai shekaru 75 yana daga cikin mutane shida da ake zargi da hada-hadar miyagun kwayoyi a wani samame da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) suka kai a wasu sassan jihar Anambra.
Har ila yau, a wani samame daban, Hukumar ta kama Alfa Andrew dan shekaru 30 biyo bayan lalata masa gonar wiwi mai nauyin kilo 178,750 a garin Mayafi, karamar hukumar Sardauna, jihar Taraba.
Yayin da aka kama Uchelue a Umudioka, karamar hukumar Dunukofia ta jihar Anambra da miyagun kwayoyi kimanin kilo 26.7 a ranar Alhamis, 28 ga Agusta, 2025; Eneh Makuo; Emmanuel Chiemeli; Uwakwe Matthew; Chukwujekwu Ehirim; Ifeanyichukwu Olisa da Odoh Chukwuma, duk suna daga cikin mutanen da NDLEA ta cika hannun da su dauke da nau’ukan miyagun kwayoyi daban-daban duk a jihar ta Anambra.
Amma Andrew na jihar Taraba, an kama shi ne a ranar Talata, 26 ga watan Agusta lokacin da jami’an NDLEA da hadin gwiwar jami’an Sojin Nijeriya, da Hukumar Tsaron Daji, da kungiyar matasan Mambila da ‘yan banga, suka kai farmaki a gonarsa mai fadin hekta 71.5 ta tabar wiwi da ke dajin Mayodoga, gundumar Mayosabere a karamar hukumar Sardauna, jihar Taraba, inda suka lalata ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp