Kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa da kuma kungiyar Editocin Nijeriya (NGE) sun maka Gwamnan Jihar Neja Umar Bago da Hukumar Yada Labarai ta Kasa a kotu kan abin da suka bayyana a matsayin tsoratarwa ga gidan rediyon Badeggi FM, Minna, da kuma barazanar rufe gidan rediyon.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar Lahadi, inda ya zargi NBC da gazawa wajen kare ‘yancin gidan rediyon.
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago
- Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Bago ya bayar da umarnin rufe tare da kwace lasisin gidan rediyon Badeggi FM 90.1 da ke Minna bisa zargin tunzura jama’a.
Gwamnan ya kuma umurci jami’an tsaro da su rufe gidan rediyon tare da nemo bayanan mai gidan rediyon, inda ya zarge ta da haddasa tashin hankali.
Sai dai a kara mai lamba FHC/L/CS/1587/2025 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Legas da SERAP da kuma NGE suna neman sani “ko a sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da sashe na 2(1) (t) na dokar NBC, NBC na da hakkin kare ‘yancin Badeggi FM da gwamnan Neja ya rufe.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp