Wata kotun majistare da ke Kaduna, ta yanke wa wani mutum Rabi’u Yusuf hukuncin daurin makonmi 16 a gidan yari bisa samunsa da laifin satar wayoyin iPhone guda biyu da kudinsu ya kai Naira 678,000.
Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya ce wanda ake tuhumar ya kasa bai wa kotun cikakken bayanin dalilin da ya sa ya aikata laifin.
- Kwamitin Tallafin Karatu Na Sanata Maidoki Ya Tantance Dalibai Sama Da 805 A Kebbi
- Ambaliya: A Hada Gwiwa Don Ceto Borno – Gwamnatin Kano
Emmanuel ya tuhumi mai laifin da ya daina aikata duk wani laifi ko kuma ya fuskanci hukunci mai tsanani idan aka sake samunsa da wani laifi a nan gaba.
Mai laifin wanda ke zaune a titin Ali Akilu a Jihar Kaduna, an same shi da laifin hada baki da sata kuma ya amsa laifinsa.
Tun da farko, mai gabatar da kara, Insifekta Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa wanda ake karar ya aikata laifin tare da hadin bakin wasu mutane biyu, a ranar 13 ga watan Satumba a Kurmin Marshi Kaduna.
Leo ya ce wanda ake tuhumar ya saci wayoyin iPhone guda biyu wadanda kudinsu ya kai Naira 678,000 daga shagon mai karar, Zainab Salisu.
Ya ce wanda ake karar da wadanda ake zargin sun zo shagon ne bisa zargin sayan kayan sawa wanda daga nan ne suka sace wayoyin iPhone guda biyu yayin da aka ajiye suna caji.
“Daga baya an gano su ta hanyar kyamarar CCTV cewa wanda ake tuhumar ne ya saci wayoyin,” in ji mai gabatar da karar.
Ya kara da cewa an gano wayoyin kuma an kama wanda ake tuhumar.
Leo ya ce laifin ya ci karo da tanadin kundin laifuffuka na Jihar Kaduna na shekarar 2017.