A yau Juma’a ne kamfanin zirga-zirgar jiragen saman fasinja na China Eastern Airlines, ya karbi jirgin sama kirar C919 da ya yi oda, wanda hakan ya sanya kamfanin na China Eastern Airlines zama na farko da ya sayi jirgin saman kirar kasar Sin.
Yayin mika sabon jirgin saman mai lamba B-919A ga kamfanin, ya kammala tashi da sauka tsakanin filin jirgin saman Pudong dake birnin Shanghai, zuwa filin jirgin saman Hongqiao na birnin Shanghai.
Bayan kamfanin na China Eastern Airlines ya amshi jirgin, zai yi gwajin sama da sa’o’i 100 na tashi da sauka ba tare da fasinjoji ba, inda zai yada zango a biranen Shanghai, da Beijing, da kuma Guangzhou.
Ana kuma sa ran fara dakon fasinjoji da sabon jirgin a lokacin bazarar shekarar 2023 dake tafe. (Saminu Alhassan)