Ta A ranar ashirin da shida ga watan satumba, shekara ta dubu biyu da ashirin da biyar (26/9/2025). Aka gudanar da bikin nadin sarautar da aka yi wa Haj. Zahra’u Sale Fantami, wacce aka fi sani da Adaman Kamaye cikin shirin Dadin kowa. Ita dai wannan sarauta an gudanar da bikin nadinta a kasar Ghana, inda jama’a ke ta rade-radi game da sarautar. Jarumar ta bayyanawa masu karatu gaskiyar magana game da wannan batu.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar Jaridar Leadership Hausa RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
- Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
- MDD Ta Yi Alƙawarin Tallafa Wa Gidauniyar Malala Mai Rajin Inganta Ilimin ‘Ya’ya Mata
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki.
Sunana Zahra’u Sale Fantami, wacce aka fi sani da Adaman Kamaye ko Adaman Na Ta’ala a cikin shirin Dadin Kowa.
Ana ta rade-radin an baki sarauta, shin mene ne gaskiyar maganar?
Alhamdulillah, maganar an bawa Zahra’u sarauta ba karya ba ne, hakkun haka ne an ba ni sarauta.
Mutane za su so su ji, shin daman Haj. Zahra’u ‘yar Ghana ce, tana da sarauta a Ghana?
A’a! Ni ba ‘yar Ghana ba ce, ba abin da na hada da Ghana, sai dai so da yarda, saboda ma’abota kallon finafinan hausa ne. Ni kuma ina cikin wannan masana’anta ta finafinan hausa, musamman Dadin Kowa na Arewa24. Alhamdulillah Arewa24 ta sa sunanmu ya tafi a duniya. Ta yi mana riga ta yi mana wando babu abin da ba ta yi mana ba, domin dalilin fuskanmu da ta tafi ake kaunar mu har ake karrama mu.
Me ya sa aka baki sarauta?
An ba ni wannan sarauta ne ba dan na gada ba, an ba ni ne a matsayin cancanta, da so da yarda da amincewa a birnin Kumasi da Accra. Na ziyarci wadannan masarautu domin karrama su da basu allon girma wato ‘Award’. Na je na gaishe su, na ziyarce su, ubangiji Allah ya sa suka ce da ni to, wannan sarki na Kumasi ya ce da ni,shi fa ba zai iya yi min komai ba sai dai ya ba ni Jakadiyarsa ta London da America, da nan Kumasi da kuma Najeriya. Haka zalika shi kuma sarkin Accra ya ba ni magajiyarsa ta London da America da Accra da kuma nan Najeriya. Alhamdulillah kuma na gode, an karrama ni kuma na ji dadi.
Me ya fi burge ki a nadin sarautar da aka yi miki?
To, Alhamdulillah ita dai wannan sarauta, sarauta ce me dadi, an ba ni kudi sannan kuma an yi min albashi. Sannan ga alfarma, alfarmar da aka yi min idan za a fita kamar turai wajen London zuwa America an ba ni alfarmar mutum uku ni ta hudu. Za a ba ni kujera mu je mu dawo duk abin da za a yi. Sannan alfarma ta biyu idan a Ghana za a yi taro an ba ni alfarmar mutum goma sha daya ni ta sha biyu, za a ba ni kujera mu je mu dawo. Dan haka wannan abun alfahari ne a gare ni.
Wane irin farin ciki ki ke ji game da wannan sarauta da aka baki?
Gaskiya na ji dadi kwarai da gaske, kuma na yi wa Allah godiya. Dan ban taba tsammanin zan taka wannan mataki ba, wanda Allah ya sa ina da rabon shi. Kuma na taka shi, komai nufin Allah ne. Mutanen Ghana sun nunan tamkar uwa daya uba daya, an karramani an mutuntani an daukake ni, ina alfahari da mutanen Ghana, sun ba ni tarihin da ba zan taba mantawa da shi a rayuwata ba.
Ko akwai wani abu da ki ke son fada wanda baki fade shi ba, game da wannan sarauta?
Ina mika sakon godiya musamman ga mai girma Alh. Ahmed Ibrahim Watara, shi ne sarkin Wangarawan Kumasi Allah ya kara masa lafiya, shi ya fara ba ni wannan mikami na Jakadiya. Shi kuma Alhaji Yahaya Hamisu Bako maimartaba (Sarkin Zangon Accra), Ghana shi kuma ya ba ni magajiya. Ina mika godiya ta musamman ga Alh. Armaya’u Sulaiman (Sarkin Daddawan Ablekuma Central), sannan shugaban matasan Bilbila. Ina mika godiya ta musamman ga sauran mukarraban fada bakidaya, ba zan iya cewa sai na kira sunan kowa da kowa ba, amma a gurguje akwai Haj. Fati Sarauniya (Sarauniyar Zangon Accra), akwai Haj. Hauwa (Majidadiyar Accra, akwai Haj. Magajiya (Magajiyar Zangon Accra), akwai Haj. Gado (Wakiliyar Bare-bari), akwai Hajiya magajiya (Wakiliyar Wangarawa), Akwai Uncle Sonihi (Sarkin Jaddada zaman lafiya na Wangarawa), Da Dan’masani (Wangarawa). Ina mika godiya ga dukkanin mukarraban wannan fada masu daraja, Alhamdulillah Ala kulli hal, ina yi wa kowa fatan alkhairi.
Me za ki ce ga masoyanki?
Ina son masoyana na fadin duniya su tayani addu’a da fatan alkhairi, da fatan Allah ya sa mu gama lafiya. Ina kira ga masoyana idan an ga zan yi abin da ba daidai ba a biyo ta social media a sanar da ni, domin in gyara. In an ga zan yi kuskure a bani shawara ta kafafen sadarwa, inda sako zai same ni cikin sauki. Makiya kuma ina so su kara sako ido saboda sai da gishirinsu muke samun suga, a fuskar makiyi muke gane aikin mu ya yi kyau ko bai ba. Allah ya karo mana dubun makiya dan mu ba ma so su yi kasa.
Wassalamu Alaikum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp