Christopher Musa Danjuma ya koma bakin aikinsa a matsayin babban kocin tawagar mata yan kasa da shekaru 20, Falconets.
Biyo bayan wata tattaunawa da kwamitin fasaha na NFF ya yi a ranar Alhamis, kwamitin gudanarwa na NFF ya amince da nadin.
- Osimhen Na Shirin Karar Napoli Kan Wani Bidiyonsa Da Suka Dora Akan TikTok
- Newcastle Ta Kori Manchester City A Gasar League Cup Ta Kasar Ingila
Danjuma, wanda ya dauki aikin wucin gadi a tawagar manyan mata ta kasa, Super Falcons sau biyu, ya jagoranci Falconets zuwa wasan kusa dana karshe na gasar cin kofin duniya na mata na FIFA U20 a bara a Costa Rica.
Gogaggen mai horarwar zai kasance tare da mataimakin mai horar da yan matan U20 da U17 Mansur Abdullahi, da tsohuwar yar wasan Super Falcons Effioanwan Ekpo.
Kungiyar Falconets za ta fara kamfen din neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta mata na ‘yan kasa da shekaru 20 na shekarar 2024 a Saint Pierre a ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba, inda za a buga wasan zagaye na biyu a filin wasa na MKO Abiola, Abuja ranar Asabar. 14 ga Oktoba, 2023.