Sarki Salman bin Abdelaziz na kasar Saudi Arabiyya, ya nada dansa, Mohammed ibn Salman a matsayin sabon Firaminista, mukamin da bisa al’ada sarkin ne ke rike da shi.
Wata sanarwar da fadar masarautar kasar ta fitar a jiya Talata da kuma kamfanin yada labaran Saudi Arabiyya ya wallafa, ta ce Mohammed bin Salman shi ne sabon Firaministan kasar.
- Buhari Ya Haramta Siyan Makamai Ga Jami’an Tsaron Sa-Kai A Jihohi
- Fitaccen Jarumin Fina-finan Hausa, Umar Yahaya Malumfashi Ya Rasu
Sabuwar dokar ta bayyana cewar, dan uwansa Yarima Khalid bin Salman zai zama ministan tsaro sakamakon garambawul din da sarkin ya sanar.
Garambawul din ya kunshi nada Yousef bin Abdullah bin Muhammad al-Bunyan a matsayin ministan ilimi, yayin da Yarima Abdulaziz bin Salman ya ci gaba da rike mukaminsa na ministan makamashi, sai kuma Yarima Faisal bin Farhan a matsayin ministan harkokin waje tare da Khalid bin Abdulaziz al-Falih a matsayin ministan zuba jari.
Yarima Abdulaziz bin Saud bin Nayef bin Abdulaziz zai ci gaba da rike mukamin ministan cikin gida, yayin da Mohammed bin Abdulahi al-Jadaan zai ci gaba da rike ministan kudi.