Jama’a da dama musamman a karamar hukumar Birnin Kano dama sauran kananan hukumomin Kano ta tsakiya na yabawa irin gagarumar gudunmawar da Ambasada Alhaji Yusuf Hasan Darma ke bayarwa ga tallafawa bunkasa ci gaban al’umma ta bangarori daban-daban.
Ambasada Yusuf Darma dan kasuwa ne da yake da tausayi da jinkai ganin irin halin kuncin rayuwa da ake ciki yake tallafa wa al’umma a fannoni da dama domin rage musu radadi da ake ciki.
- Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ba Za Ta Samu Wani Sabon Bashi Daga Bankin AfDB Ba -Farfesa Oyebanji
- Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ba Za Ta Samu Wani Sabon Bashi Daga Bankin AfDB Ba -Farfesa Oyebanji
Mutum ne da yake ba da tallafi ga kungiyoyi da daidaikun mutane maza da mata kamar yanda wani dan kasuwa Alhaji Abubakar Kanabaro ya bada irin wannan kyakkyawan shaida akansa bayan wani rabon tallafi da ya yi a Kumbotso.
Alhaji Yusuf Hasan Darma sannanne ne akan irin gagarumar gudummawa da ya bayar domin tabbatar da samun nasarar Abba Kabir Yusuf da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam tun daga zaben 2019 har zuwa na 2023 karkashin jam’iyyar NNPP ya bada gudunmawa ga tun daga yakin neman zabe da lokacin zabe har kaiwa ga nasara, kuma ya bada gudunmawa wajen tsayin dakan ganin anyi nasara a kotu tun farkon Shari’a har aka tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf.
Mutane da dama yan siyasa da sauran al’umma da suka sani suke ganin irin gudunmawa da Yusuf Hasan Darma ya ke bayarwa suna kira ga Gwamnatin Jihar Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakin sa Kwamared Abdussalam Abubakar da Madugun Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suyi duba da lura da irin gudunmawa da wannan bawan Allah Yusuf Hasan Darma yake bayarwa da aljihunsa domin irinsu yakamata a jawo su a jiki su bada gudunmawa wajen gudanar da Gwamnati duk abinda za’ayi na al’umma a damka musu saboda sako zai je ko’ina.
Ba kadai tallafi ga mutane ba Alhaji Yusuf Hasan Darma ya ba da tallafi wajen sanya fitilu a mazabu 13 na karamar hukumar Birnin Kano sannan yana raba tallafi ga mata da matasa da tallafawa harkar Ilimi a makarantu da biya wa dalibai kudin jarabawa.
Malam Aliyu Mamman Mai mari daya daga wadanda kungiyar sa ta amfana da tallafi na N500,00 daga Alhaji Yusuf Hasan Darma ya ce bashi kadai ba, akwai kungiyoyi da dama makamantan nasa da suka amfana da tallafin da a cikin ikon Allah zai basu dama na cika burin abinda suka sa a gaba na tallafawa al’umma suma.
Jama’a dai da dama suna ta Karaye kiraye ga shugabanni, musamman Gwamnatin jihar Kano da sauran jagorori musamman da yake sun san wanne Ambasada Yusuf Hassan Darma da irin gudunmawa da yake bai wa al’umma da ga aljihunsa, ba tare da yana rike da wani mukami a gwamnati ba, suna jan hankali akan a duba irin hidima da yake a bashi wani gwaggwabar mukami da zai dada karfafar sa wajen taimakawa ci gaban al’umma da yake.