Shugaban kungiyar masu sayar da ganye da kayan marmari na Kasuwar Utako Babban Birnin Tarayya Abuja Mu’azu Hamza Karwai ya nuna jin dadinsa kwarai dakan yadda gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Yusuf ke taimakawa ɓangaren ilimi, ya ce sun san dama can yana niyyar yin hakan shi yasa ma suka zabe shi domin sun ba zai basu kunya ba. Ko yanzu ma duk dan Jihar Kano da sauran ‘yan Nijeriya sun ce alhamdu lillahi sun san ba za su yi zaben tumun dare ba ko dana-sani kan zabn shi ba, don haka suna yi ma shi fatan alkhairi a kowane lokaci.
Ya ce sun godewa Allah domin burinsu ya cika, bada dadewa bane gwamnatin ta Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamnan Kabir Yusuf ta dauki nauyin karatun dalibai ‘yan asalin Jihar Kano 590 wajen yanke shawarar tura su karatu zuwa kasashen waje da kuma wasu makarantun na cikin gida Nijeriya, don haka wani abu ne na ayaba kwarai da gaske.
Saboda ai ilimi shi ne gishirin zaman duniya duk wani ci gaba ta fanon daban- daban sai da ilimi ake yin samun shi, don haka shi yasa, abinda yake yi, musamman ma yadda ya maida hankali kan lamarin daya shafi ilimi.
Bugu da kari ya ce samun jajirtaccen gwamna irin na Kano wani abu ne mai wuya,musamman ma yadda ya dauki mataki na sai ma jami’an tsaro abubuwan da za su taimaka masu wajen sayen Motoci, da Babura da za’ayi amfani da su domin tunkarar matsalar tsaro da ta fara kunno kai ta Jihar Kano, shi ma wannan matakin abin a yaba ne matuka domin shi lamarin tsaro babu wanda zai yi ma shi rikon sakainar kashi. Ya ce ya kara yabawa da jinjina ma shi kan yadda ya maida hankali yanzu ga Lafiya, tsaro da kuma ilimi.
Sai dai duk hakan ya yi kira da gwamnan ya maida hankalinsa wajen tunawa da lamarin da ya shafi hanyoyin mota, alal misali kamar hanyar Bunkure ta zuwa mazabarsa, yana kuma fatan sauran fannoni kamarsu hanyoyi da saurana wasu ayyuka a tuna da kauyuka, suma duk cikin Jihar ta Kano suke, duk da yake an san baya wai baya manta bane amma ana kara tuna ma shi suma mutanen karkara a tuna da su. Yana yi ma shi fatan Allah ya ci gaba da taimaka masa ci gabansa, Jihar Kano da kuma Nijeriya baki daya.














