Dan majalisar dokokin jihar Adamawa, mai wakiltar karamar hukumar Hong, Honarabul Batiya Wesley, ya zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar.
Mambobin majalisar sun zabi Honarabul Batiya ne ranar Talata a zauren majalisar ta takwas, ba tare da hamayya ba.
- Bilyaminu Ismail Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Zamfara Karo Na 7
- Lawan Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Borno Karo Na 4 A Jere
Haka kuma mambobin majalisar sun zabi mamba mai wakiltar Jada-Mbulo, Honarabul Buba Muhammad Jijiwa, a matsayin mataimakin kakakin majalisar ba tare da kai ruwa rana ba.
Dama dai kakakin majalisar dokokin da mataimakinsa, ba su tsaya takara ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp